Bello Turji Ya koma Sabon Mafaka Bayan Hare-Haren Sojoji
Hukumar tsaro ta Najeriya ta kara tsaurara matakan farmaki kan hatsabibin dan ta'adda, Bello Turji, wanda aka gano yana hijira a sabbin wurare bayan hare-haren da sojoji suka kai masa a jihar Zamfara. An bayyana cewa, Turji ya koma sabon mafaka a gabashin Dutsin Birnin Yaro don tserewa daga tsauraran farmakin da sojoji suka kai a yankin Fakai.Rahotanni sun tabbatar da cewa, Bello Turji ya sauya wurin ajiyar wadanda ya sace zuwa dazukan Dajin Jajjaye, Zaman Gira, Birnin Yaro, da Dogon Karfe. Sabbin 'yan bindiga sama da 100 sun raka wadanda aka sace, suna daukar matakan tsaro a hanyar Kwanar Jalop dake tsakanin Jangeru da Birnin Yaro.Hare-haren da sojoji suka kai sun jawo mummunan illa ga Turji, wanda yanzu haka ke neman mafita daga dakarun tsaro. A kwanakin baya, dakarun sojojin sun ruguza ...








