Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Biliyan 33.45 Don Ayyukan Ci Gaba
Gwamnatin jihar Kano ta amince da ware Naira biliyan 33.45 domin gudanar da muhimman ayyuka da zasu inganta rayuwar al'umma a fannonin ilimi, kiwon lafiya, da more rayuwa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan a taron majalisar zartarwa da aka gudanar ranar Laraba.
Ayyukan da za a aiwatar da wannan kuɗi sun haɗa da gina tituna, asibitoci, makarantu, da gidaje, duk da nufin inganta walwalar al’ummar jihar. Kwamishinan labarai, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wannan mataki na nufin inganta harkokin ci gaba a jihar.
Gwamnatin ta ware N426.4 miliyan don biyan hakkokin masu share titi 2,369 na tsawon wata tara, tare da N109 miliyan da za a yi amfani da su wajen sayen JAMB ga daliban jihar. Hakanan an ware N284.1 miliyan don gina sabon asibiti na zamani a yankin Rimin Z...








