Taron Shugabannin APC a Abuja: Tinubu Ya Jagoranci Taron Mashawarta
A yau, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar mashawartan jam’iyyar APC a fadar gwamnatin Aso Rock da ke Abuja. Wannan taro na farko ne da aka gudanar tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. Taron ya samu halartar shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da gwamnonin jihohi, ministoci, da tsofaffin gwamnonin APC.Taron ya zo ne a cikin sa'o'i 24 bayan furucin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya ce zai fice daga APC idan jam'iyyar ba ta gyara kanta ba. Wannan ya jawo hankalin shugabannin jam'iyyar, wanda hakan ya sa su taru domin tattauna matakan da za a dauka don inganta jam'iyyar.A cikin taron, an tattauna batutuwa da dama, ciki har da shirin gudanar da babban taron jam'iyya na NEC a hedikwatar APC da ke Wuse 2, Abuja. Daga cikin shug...








