
Ƴan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matafiya a Hanya, ‘Yan Sanda Sun Dauki Mataki
Ƴan bindiga sun tare wata motar haya a jihar Benue, inda suka yi garkuwa da matafiya. Wannan lamarin ya faru ne a yankin Ikobi, inda Ƴan bindigan suka hallaka direban motar da wani fasinja a kujerar gaba.Bayan faruwar wannan mummunan lamari, jami'an rundunar Ƴan sanda sun gudanar da gaggawar ceto tare da samun nasarar kuɓutar da fasinjoji 14 da aka sace. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin su.Jami'an tsaro suna ci gaba da bin sawun Ƴan bindigan a cikin daji, yayin da ake ƙoƙarin dakile mummunar ta'addanci a jihar. Wannan lamari ya jawo hankalin hukumomi kan tsaro a yankin, musamman a lokacin bukukuwan Sallah.