Kwankwaso Ya Samu Lambar Yabo Daga Kungiyar Matasa a Najeriya
A wata babbar katafaren taro da aka gudanar a Jihar Kano, kungiyar Arewa Youth Democratic Movement ta karrama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da lambar yabo a matsayin jagoran da ya fi bayar da gudunmawa a bana. Wannan karramawa ta zo ne bayan irin kokarin da Kwankwaso ya yi wajen tallafawa matasa da kuma ci gaban al'umma.Shugaban kungiyar, Muhammad Sabo Bakin Zuwo, ya bayyana cewa Kwankwaso ya cancanci wannan yabo saboda irin gudunmawar da yake bayarwa a fannoni da dama, musamman a bangaren ilimi da sana'o'i. Ya ce, "Sanata Kwankwaso jagora ne wanda ya taka rawar gani wajen bunkasa rayuwar matasa a Najeriya."Bayan bayar da wannan lambar yabo, jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan cancantar Kwankwaso, inda wasu suka yi imanin cewa zai iya zama shugaban Najeriya a zaben 2027. Wani mai suna...








