Rikicin Zanga-Zangar Matasan Abuja: ‘Yan Sanda Sun Tsunduma
A ranar Laraba, 5 ga Maris, 2025, 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zanga a gaban majalisar tarayya a Abuja. Wannan zanga-zanga ta biyo bayan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, na neman ta da lalata.Matasan sun hallara a kofar majalisar tun da misalin karfe 8 na safe, suna dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce kamar "Dole ne Akpabio ya sauka" da "Kare hakkin mata". Wannan zanga-zanga ta jawo hankalin jami'an tsaro, wanda hakan ya sa aka tura 'yan sanda, NSCDC, da sojoji wurin domin hana tashin hankali.Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda ba su yi jinkirin harba hayaƙi mai sanya hawaye ba, wanda ya tilasta wa masu zanga-zangar tsere daga wurin. Bayan tarwatsawa, sun koma bangaren Unity Fountain inda ...








