Anyi Babban Rashi: Tsohon Hadimin Shugaban Najeriya ya rasu
A ranar Juma'a, 7 ga watan Maris, 2025, Najeriya ta yi rashi da Dr. Doyin Okupe, tsohon hadimin shugabannin kasa, wanda ya rasu yana da shekara 72. Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya shafe shekaru 16 yana fama da ciwon daji, wanda ya kai ga bukatar tafiwa Isra’ila don samun magani.Dr. Okupe, wanda ya fito daga garin Iperu a jihar Ogun, ya yi fice a fannin siyasa da kiwon lafiya. Ya kasance likita mai hazaka wanda ya kafa cibiyar kiwon lafiya ta Royal Cross a jihar Legas tare da wasu abokansa likitoci. A lokacin jamhuriya ta uku, ya zama mai magana da yawun jam’iyyar NRC, sannan ya yi aiki a matsayin hadimin shugabannin Najeriya da suka hada da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.A shekarar 2022, Okupe ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar LP, amma daga baya y...








