Tinubu Ya Yaba wa Osinbajo a Ranar Haihuwarsa
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 68, inda ya bayyana godiya ga gudunmawar da ya bayar a lokacin mulkinsa.A wani taron da aka gudanar, Tinubu ya jaddada irin rawar da Osinbajo ya taka wajen ci gaban Najeriya, musamman lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Muhammadu Buhari. Shugaban ya kuma tuna da kwarewar Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a lokacin da Buhari ke jinya a Birtaniya, inda ya jagoranci al’amuran kasa da hikima.Tinubu ya bayyana cewa Osinbajo yana da 'yancin tsayawa takara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a 2023, yana mai cewa har yanzu aboki ne a tafiyar siyasa. A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Dada Olusegun, ya wallafa, Tinubu ya yi addu'o'i ga ...








