Asalin Kungiyar Lakurawa da Yadda Suka Shigo Najeriya
An gano cewa kungiyar Lakurawa, wacce ta shahara wajen aikata ta'addanci a arewacin Najeriya, ta fara ne a shekarar 1997 a Nijar, a karkashin shugabancin Ibrahim Baré Maïnassara. An kafa kungiyar ne don kare makiyaya daga hare-haren ‘yan fashi da ke yawan kutsawa daga Mali.A lokacin, 'yan fashi suna yawan satar dabbobi, wanda hakan ya jefa makiyaya cikin hatsari. Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar kafa kungiyar Lakurawa domin tunkarar wannan barazana. An bai wa mambobin kungiyar horo na soja da makamai domin tabbatar da tsaro a yankin.Bayan nasarorin da Lakurawa suka yi wajen fatattakar ‘yan fashi daga Nijar, Shugaba Baré ya fadada shirin, inda aka kafa karin sansanonin horo a wasu wurare. Duk da haka, bayan rasuwar Shugaba Baré a shekarar 1999, makomar kungiyar ta fara zama mai cike da ras...








