Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Tsarin Rage Farashin Kayan Abinci
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da matakin da ta ɗauka na rage farashin kayan abinci a jihar, musamman a lokacin azumin Ramadan. Gwamna Ahmad Aliyu ya bayyana cewa wannan shiri na rage farashi ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla da ƙungiyar dillalan kayayyaki.Gwamnan ya ce: "Mun kulla wannan yarjejeniya ne domin tabbatar da cewa al'umma za ta samu kayan abinci a farashi mai rahusa, musamman a wannan wata mai alfarma." A ƙarƙashin wannan tsarin, gwamnatin za ta ba da tallafin kuɗi ga dillalan kayayyaki domin rage farashin.Wannan mataki na gwamnatin Sokoto yana da nufin sauƙaƙa wahalhalun da jama'a ke fuskanta, musamman a lokacin azumi, inda mutane da yawa ke fuskantar matsalolin tsadar kayan abinci. Gwamnatin ta tabbatar da cewa wannan yunƙuri zai taimaka wajen inganta jin daɗin al'umma...








