
Nuhu Ribadu Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen Kisan Gilla a Jihar Filato
A yayin ziyarar da ya kai a jihar Filato, Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankin. Ribadu ya bayyana cewa, hare-haren da suka afku a ƙaramar hukumar Bokkos sun jawo asarar rayuka da dama, inda aka kashe akalla mutum 50.Ribadu ya yi kira ga al’umma da su haɗa kai da gwamnati domin yin aiki tare wajen magance wannan matsala ta rashin tsaro. Ya jaddada cewa lokaci ya yi da al’umma za su ɗauki matakan kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakaninsu.Hakanan, ya bayyana cewa duk da kokarin da dakarun tsaro ke yi, haɗin kai tsakanin al’umma da gwamnati yana da matuƙar muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya. Ribadu ya yi kira ga jami'an gwamnati da su ɗauki matakan gaggawa don magance wannan rikici da ke ci gab...