Sheikh Gumi Ya Mayar da Martani Kan Maganganun El-Rufa’i
Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi martani mai zafi kan sauya shekar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zuwa jam’iyyar SDP. Gumi ya bayyana cewa El-Rufa’i ya yi maganganu marasa dadi a baya, kuma yanzu ya kamata ya fuskanci abin da ya aikata lokacin yana kan mulki.A cikin wata hira da aka yi da Gumi, ya ce, "El-Rufa’i ya yi rushe-rushe da zaluntar mutane, amma yanzu da aka kwace mulki a hannunsa, sai ya dawo yana kuka." Malamin ya bayyana cewa wannan canji daga mulki zuwa zama ɗan adawa yana zama darasi ga sauran shugabanni masu girman kai a Najeriya.Gumi ya yi nuni da cewa a lokacin da El-Rufa’i ke kan mulki, bai kula da ra'ayoyin mutane ba, kuma yana fatan hakan zai zama wa'azi ga dukkan shugabannin da suke rike da karagar mulki. Ya ƙara da cewa, "Matsalar shuga...








