
Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Sace Farfesa da Fasinjoji
A ranar Lahadi, 2 ga Maris, 2025, wasu ƴan ta'adda da ake zargin suna daga cikin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun kai hari a jihar Borno, inda suka yi awon gaba da Farfesa Abubakar Eljuma daga jami'ar sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB) tare da wasu fasinjoji.An sace Farfesan tare da fasinjojin a kan titin Maiduguri-Damaturu, kusa da ƙauyen Kamuya, wanda ke fama da matsalar tsaro. Rahotanni sun tabbatar da cewa Farfesa Eljuma, wanda ke takara don zama shugaban jami'ar NAUB, na daga cikin wadanda aka sace.Wannan lamarin ya faru ne a kan titin Damaturu-Biu, wanda a ka saba samun hare-hare daga ƴan ta'adda. Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun sace matafiya da suka yi tafiya a cikin motocin su, inda an sace maza da mata.Duk da cewa an sako dukkan matan da ke cikin motocin, maza guda sun...