Sojoji Sun Yi Nasara Kan Ƴan Ta’addan Lakurawa a Jihar Kebbi
Dakarun soji a jihar Kebbi sun yi artabu da ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa, wanda ya haifar da asarar rayuka da kuma kwato makamai masu yawa. Wannan samamen ya gudana ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta'addan.Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartaswa ta jihar Kebbi, AbdulRahman Zagga, ya bayyana cewa sojojin sun hallaka mambobin ƙungiyar guda biyu a yankin Rubin Bisa da Fana, a cikin ƙaramar hukumar Dandi. Ya ce, “Mun samu nasarar kashe ƴan ta'addan bayan samun bayanai daga rahotannin leƙen asiri.”Zagga ya bayyana cewa wasu daga cikin ƴan ta'addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka ƙwato makamai da dama daga hannunsu, ciki har da bindigogi na zamani da alburusai. Wannan samamen ya biyo bayan koke-koken shugaban ƙaramar hukumar Dandi, Dokta Mansur Kamba, kan a...








