Kasuwa ba Tabbas: Wasu Ƴan Najeriya Sun Tafka Asarar Naira Tiriliyan 1.4 a Mako 4
Kasuwar hannun jari ta Najeriya (NGX) ta fuskanci asarar Naira tiriliyan 1.4 a cikin makonni hudu, wanda ya sa jimillar jarin kamfanoni ya ragu zuwa Naira tiriliyan 65.819. Ma'aunin hannun jari na ASI ya ragu da kashi 2.7%, yana nuna ci gaba da faduwar kasuwa duk da saukar farashin kayayyaki a Najeriya.A ƙarshen ranar Juma'a, jimillar jarin kamfanonin da aka yi hada-hadarsu ya ragu daga Naira tiriliyan 67.193 zuwa Naira tiriliyan 65.819, daidai da ragin kashi 2.1. Masu saka hannun jari suna fuskantar fargabar lalacewar kudaden su, yayin da masana ke ganin wannan babbar dama ce ta sayen hannun jari a farashi mai sauki.Kasuwar ta ragu sosai, inda jimillar hannun jarin da aka sayar a mako ya sauka da kashi 11.5% zuwa Naira biliyan 2.90. Jimillar kuɗin da aka samu a hada-hada ya ragu da kashi ...








