
Gwamna Ya Haramtawa Malamai yin Wa’azi a Kasuwanni
Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, ya sanar da haramta wa'azi a kasuwanni a jihar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin rage hayaniya da gurbatar iska da wa'azinta ke jawo wa.A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, Soludo ya bayyana cewa duk malamin addini da aka kama yana wa'azi a kasuwa zai biya tarar N500,000. Wannan mataki ya jawo cece-kuce daga shugabannin addini, wadanda suka yi kira da cewa wannan haramta cin zarafin 'yancin addini ne.Shugaban kungiyar Bishops na kasa da kasa, Archbishop Osazee Williams, ya bayyana cewa haramta wa'azi a bainar jama'a yana hana mutane jin kalmar Allah, wanda ke da matukar muhimmanci ga al'umma. Ya kara da cewa wa'azi a kasuwanni na iya canza halayen mutane da kuma inganta zamantakewar al'umma.Haka zalika, shugaban cocin Metho...