
Farashin Abinci da Fetur Ya Ragu a Najeriya: Minista Ya Bayyana Nasarorin Gwamnati
Ministan Sadarwa da Wayar da Kan 'Yan Kasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa sun fara nuna tasiri mai kyau a Najeriya, inda farashin abinci da man fetur suka ragu. A yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, Idris ya jaddada cewa wannan ci gaba na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa.Ministan ya bayyana cewa, bayan aiwatar da manufofin gwamnati, an samu raguwar wahalhalu da dama da 'yan Najeriya ke fuskanta. Ya yi nuni da cewa, "Mun tsallake mawuyacin hali, kuma wahalhalun da ke tattare da sauye-sauyen suna raguwa yayin da sakamakon ke fara bayyana."Idris ya kuma yi kira ga shugabannin addini da su yi addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa. Ya bayyana cewa, duk da cewa sauye-sauyen na iya fuskantar adawa, ...