Gwamna Okpebholo Ya Kai Ziyara ga Sanata Barau kan Kisan Hausawa
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ta’aziyya ga Sanata Barau Jibrin a gidansa da ke Abuja, domin nuna alhini kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a Uromi, Jihar Edo. Wannan ziyara ta biyo bayan mummunan lamarin da ya jawo hankalin al'umma da dama.A lokacin ziyarar, Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa an cafke mutane 14 da ake zargi suna da hannu a cikin wannan kisan. Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tallafawa iyalan wadanda suka rasa ransu a wannan mummunan lamarin. Haka zalika, ya bayyana cewa akwai bukatar a hukunta duk wadanda suka aikata wannan aika-aikar domin tabbatar da adalci.Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ɗan asalin Kano ne, ya yi kira ga hukuma da ta tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Ya bayyana cewa ba za a iya canza abin da ya faru ba, a...








