
Ali Nuhu Ya Gargadi Jarumar kannywood Kan Zana Tattoo
Shahararren jarumi a masana'antar Kannywood, Ali Nuhu, ya gargadi jarumar Surayya Aminu, wanda aka fi sani da Rayya Kwana Casa'in, kan shirin da take yi na zana tattoo a jikinta. A cikin wata tambaya da ta yi wa masoyanta, Rayya ta nuna sha'awarta game da zana tattoo, wanda hakan ya jawo martani daga Ali Nuhu.Ali Nuhu ya bayyana cewa idan Rayya ta kuskura ta zana tattoo, zai sanya bulala ya zane ta. Wannan gargadi na Ali Nuhu ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin abokan sana'ar jarumar da masoyanta, inda da dama suka yi Allah wadai da wannan yunkuri.Rayya ta yi tambayar a shafinta na Instagram, inda ta nemi ra'ayin masoyanta kan zana hoton tattoo a jikinta. Wannan tambayar ta jawo muhawara mai zafi daga 'yan Kannywood da suka bayyana rashin jin dadin su game da wannan yunkuri.Daga cikin wadanda s...