
An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila da Hezbollah
Amurka ta sanar da cewa Isra'ila ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan Hezbollah da ke Kudancin Lebanon. Wannan yarjejeniyar ta biyo bayan shafe sama da shekara guda ana musayar wuta tsakanin dakarun Isra'ila da Hezbollah.
Shugaban Amurka, Joe Biden, ya bayyana cewa za a samu tsagaita wuta na tsawon watanni biyu, wanda zai ba da damar dakarun Isra'ila su janye daga Kudancin Lebanon, yayin da sojojin Lebanon za su mamaye wuraren da Hezbollah ke da iko.
A martanin sa, shugaban Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sojojinsa ba za su bata lokaci ba idan Hezbollah ta saɓa yarjejeniyar. Har yanzu, ba a ji daga kungiyar Hezbollah kan wannan yarjejeniyar ba, amma ba a sami wani alamar karya yarjejeniyar ba.
Wakilin Amurka, Amos Hochstein, wanda ya jagoranci tattaunawar, ya bayyana...