
Addu’ar Samun Ciniki: Neman Albarka da Samu ta Halal
A yau, muna kawo muku addu'ar samun ciniki, wacce take cike da hikima da kuma ma'anoni masu zurfi. Wannan addu'a tana koyar da mu muhimmancin neman albarka kasuwanci, da kuma neman halal da guje wa haram
Addu'ar:
اللَّهمَّ اكْفِني بحلالِكَ عَن حَرَامِكَ، وَاغْنِني بِفَضلِكَ عَمَّن سِوَاكَ
Ya Allah! Ka wadatar da ni daga abin da Ka halatta, domin in guji abin da Ka haramta, kuma Ka ba ni ikon dogara da falalarKa, in guji komai sai Kai."
wannan addu'a tana nuni da abubuwa masu muhimmanci game da neman taimako daga Allah da kuma bukatar kulawa da aikata Ayyuka masu kyau.
Hikimar Addu'a:
Wannan addu'a tana da hikimomi da yawa, ciki har da:
Neman Abin da Ya Halatta: Mai addu'a na neman isasshen abin da Allah ya halatta, wanda ke nuna bukatar samun abinci, kayan more rayuwa, da dukkan a...