Addu’ar Samun Basira: Hanya Mai Sauƙi don Ƙarfafa Ƙwaƙwalwa da Fahimta
A yau muna kawo muku Addu'ar samun Basira,Shifa basira tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan adam, musamman wajen koyon ilimi, fahimtar al’amura, da yanke shawarar da ta dace. Duk da yake Allah ne ke bayar da basira ga wanda Yake so, akwai hanyoyi da dama da Musulunci ya koyar domin neman wannan baiwa daga Ubangiji.Mece Ce Basira?Basira ita ce hikima da fahimta ta musamman da mutum yake da ita wajen nazarin al’amura da yanke hukunci mai ma’ana. Basira tana haɗawa da:
Fahimtar al’amura cikin sauƙi.
Iya warware matsaloli cikin hikima.
Yin tunani mai zurfi da nasara wajen koyon ilimi.
Samun ilimi da amfani da shi cikin hikima
Addu’o’i Don Neman Basira
Annabi Muhammad (SAW) ya koyar da mu wasu addu’o’i domin neman basira daga Allah. Ga wasu daga cikin su:
Addu’a ta Fa...








