Adduar kariya Daga makiya
Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu barkan mu da war haka, Ina muku maraba da ziyartan wanan blog dinmu, yau mauduin Zai kasance akan Addu'ar kariya Daga makiya
A rayuwar mu ta yau da kullum, mu kasance masu fuskantar kalubale da dama, ciki har da barazanar makiya. Makiya na iya zama daga cikin mutane ko kuma mugayen abubuwan dazadu iya shafar lafiyarmu, dukiya, da zamantakewar mu. Saboda haka, addu'a na da matukar muhimmanci wajen samun kariya daga irin wannan barazana.
Mece Ce Addu'a?
Addu'a ita ce hanyar da Dan Adam ke ni Dan ya sadu da Ubangiji Allahu SWT, inda muna neman taimako, kariya, da tsari daga gare Shi. A cikin Al-Qur'ani Mai girma da Hadisin Sunnah, an karfafa yin addu'a a duk lokacin da muke fuskantar Wata wahala ko barazana. Addu'a na iya zama ga mutum day...








