Buhari Ga Tinubu: Shugabanci Nauyi Ne, Aiki Tukuru Yake Bukata

Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki, tare da jaddada cewa shugabanci aiki ne mai bukatar juriya da kuma goyon bayan al’umma.  A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, Buhari ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke kokarin kawo wa kasar nan na bukatar lokaci da kuma hakurin al’umma.

Buhari ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su baiwa gwamnatin APC cikakken goyon baya domin cimma manufofinta na ciyar da kasar nan gaba. Ya kara da cewa, sauye-sauye ba abu bane da za’a iya gani a rana daya, illa dai a hankali a hankali.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi kira da a kaucewa sukar gwamnati ta hanyar da zata kawo tarnaki ga cigaban kasar nan. Ya bayyana goyon bayansa ga kokarin da gwamnatin ke yi na rage radadin talauci da tsadar rayuwa, wadanda suka fi shafar talakawa.

Buhari ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu kyakkyawan fata game da makomar kasar nan, tare da yin kira ga al’umma da su baiwa gwamnati lokaci domin gudanar da ayyukanta.  “Kada mu dora wa gwamnati nauyin da ya fi karfinta,” inda ya kara da cewa, “Ina taya Shugaba Tinubu murna da cika shekaru biyu a kan mulki. Allah Ya ba shi hikima da jagoranci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *