Buba Galadima Ya Zargi An So Rufe Sanusi II a Abuja

Buba Galadima na jam’iyyar NNPP ya zargi wasu da ƙulla makircin tayar da zaune tsaye a Kano domin tilasta gwamnatin tarayya ayyana dokar ta-baci. Ya bayyana cewa an shirya hakan ba tare da sanin Shugaba Bola Tinubu ba, inda aka tsara damƙe Sarkin Kano da ayyana sarautar a matsayin babu mai ita.

Galadima ya ce an yi taro a Abuja domin haddasa rikicin siyasa da zai hana zaman lafiya a jihar. Ya bayyana cewa an shirya tura wanda ake shirin nadawa sarki zuwa Umrah a Saudiyya domin kada ya kasance a cikin rikicin.

Ya kuma bayyana cewa akwai shirye-shiryen kai wa masarautar jihar hari ta hanyar ɗaukar matakan hana zaman lafiya, wanda zai ƙirƙiri dalilin ayyana dokar ta-baci. Buba Galadima ya yi wannan jawabi a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar AIT.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *