
A ranar Laraba, 5 ga Maris, 2025, fitaccen dan siyasa, Injiniya Buba Galadima, ya yi gargadin cewa saukar farashin abinci da ake fuskanta a halin yanzu na iya haifar da matsaloli masu yawa a nan gaba. A cewarsa, shigo da kayan abinci daga kasashen waje na iya durkusar da manoman Najeriya da kuma kasuwancin sarrafa abinci.
Galadima, wanda makusancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne, ya bayyana a wata hira da DCL Hausa cewa matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka na rage farashin abinci ba za su kawo ci gaba ba. Ya yi nuni da cewa shigo da kayan abinci daga ketare zai jefa Najeriya cikin mawuyacin hali na dogaro da abinci daga waje.
Buba Galadima ya ce, “Maimakon shigo da kayan abinci daga ketare, gwamnati ta kamata ta karfafa wa manoman cikin gida gwiwa ta hanyar samar musu da kayan noma na zamani.” Ya bayyana cewa wannan matakin na shigo da abinci zai jawo babbar matsala ga masana’antun sarrafa abinci a Najeriya, wanda hakan zai iya sa su fuskanci gazawa.
Galadima ya jaddada cewa, idan aka ci gaba da shigo da abinci daga waje, manoman Najeriya za su gaza samun damar yin noman da zai rage farashin kayan abinci a cikin gida. Ya ce, “Abu na farko shi ne, gwamnati ta zage damtse, ta koya wa manoma yadda ake noma irin na zamani.”
Gargadin Buba Galadima yana zuwa ne a lokacin da ake fuskantar canje-canje a kasuwar abinci a Najeriya, wanda ya jawo hankalin al’umma da dama, suna sa ran ganin matakai masu inganci daga gwamnatin tarayya.