
Ƙungiyar ‘Obidient’ Ta Ce Wa APC: Ba Za Ku Iya Lashe Zaɓe Mai Gaskiya A Najeriya Ba
Ƙungiyar 'Obidient' a Jihar Delta ta bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba za ta iya lashe ko wane irin zaɓe mai gaskiya a Najeriya ba, saboda ƙarancin ayyukan da jam'iyyar ta yi a ƙasa da kuma ƙaruwar rashin jin daɗin jama'a.Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a karshen mako a Asaba, Shugaban Majalisar Dattawa na 'Obidients' a Delta, Cif Chris Boise, ya yi watsi da sauya shekar da wasu mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi zuwa APC a jihar, yana mai cewa matakin ba zai shafi siyasar Delta ba.Ya ce: "Ba mu damu ko kaɗan game da haɗewar 'yan PDP zuwa APC. Dalilinsu na cewa wannan sauya shekar zai haifar da ci gaba ba shi da tushe idan aka yi la'akari da mummunan mulkin APC a matakin ƙasa a cikin shekaru goma da suka gabata."Boise...