
Matasan Neja Delta Sun Goyon Bayan Haɗin Gwiwar Peter Obi da Gwamna Bala
Matasan yankin Neja Delta na Kudancin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga shirin haɗin gwiwar Peter Obi da Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, a matsayin wani muhimmin mataki na kawo canji a siyasar Najeriya. Wannan goyon baya ya fito daga kungiyar matasan yankin, wato Neja Delta Youth Council (NDYC).Shugaban NDYC, Israel Uwejeyan, ya bayyana cewa haɗin gwiwar Obi da Gwamna Bala na da matukar amfani ga ci gaban Najeriya, duba da kwarewar da kowanne daga cikinsu ya samu a harkokin shugabanci. Ya bayyana cewa wannan haɗaka ta na da burin tabbatar da hadin kai da kuma kawo sauyi mai ma'ana a cikin al'umma.Uwejeyan ya jaddada cewa Gwamna Bala ya kasance mai himma wajen ganin an inganta haɗin kan ƙasa, yayin da Peter Obi ya zama abin misali a fannin shugabanci da tattalin arziki. Kungiyar t...