
Fargaba a Kano: Ana Tsoron Watsa Dokar Ta Bacin a Jihohi
Hajiya Naja'atu Muhammad, fitacciyar 'yar gwagwarmaya a siyasance a Arewacin Najeriya, ta bayyana damuwarta game da yiwuwar gwamnatin Bola Tinubu ta watsa dokar ta baci a wasu jihohi, musamman ma jihar Kano. Ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin mamaye wasu jihohi don baiwa Tinubu damar ci gaba da mulki bayan wa'adin farko.Naja'atu ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da ta yi da tashar Premier Radio, inda ta bayyana cewa bayan samun nasara a jihar Rivers, gwamnatin Tinubu na fuskantar barazana ga zababbun shugabannin jihohi. Ta yi zargin cewa akwai wasu jihohi da gwamnatin tarayya ke son mallaka domin cimma burinta na siyasa.Ta ce: "Kano ma abin da suka so su yi ke nan. Idan ka na jin labarin yadda ake zuzuta rigima a kan sarakuna, waye ke tayar da rigima? Waye ya damu, alhalin mutanen K...