
Gwamnoni Na Matsawa Tinubu Kan Ƴancin Kananan Hukumomi
An gano cewa gwamnonin Najeriya suna ƙoƙarin hana aiwatar da hukuncin da ya ba kananan hukumomi 'yancin cin gashin kai da kuɗinsu kai tsaye. A wani taro da suka gudanar da shugaban ƙasa Bola Tinubu, gwamnoni sun nuna rashin amincewa da tsarin tura kuɗi kai tsaye daga gwamnatin tarayya zuwa asusun kananan hukumomi ta hanyar CBN.Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnoni sun nemi a rika tura kuɗi zuwa bankunan kasuwanci maimakon CBN, wanda ke ƙarƙashin hukuma. Wannan mataki yana nufin cewa suna son a dakatar da tsarin har sai an biya basussukan da ake bin kananan hukumomi.A ranar 11 ga Yuli, kotun koli ta yanke hukuncin cewa ya zama dole a rika biyan kuɗin kananan hukumomi kai tsaye, wanda hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin gwamnonin. Alkalai sun bayyana cewa gwamnoni ba za su iya rike kuɗin kananan...