
Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar Ya Rasa Mahaifiyarsa a Borno
An shiga cikin yanayi na jimami a Maiduguri, birnin jihar Borno, bayan rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin Musulunci, Farfesa Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar. Sanarwar rasuwar ta fito ne daga shafin Facebook na malamin, inda ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta rasu bayan fama da jinya.Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'iza a ranar Asabar, 22 ga Maris, 2025, a babban masallacin 505 da ke Maiduguri, da misalin karfe 10:00 na safe. A cikin sanarwar, Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar ya bayyana cewa, "Innalilahi wa'inna ilahi raji'un. Mahaifiyata ta rasu, za a yi sallar jana'izarta yau."Majiyoyi sun ce an gudanar da jana'izarta kamar yadda aka tsara, tare da halartar mutane da dama daga cikin al’umma. Wannan lamari ya jawo hankalin mutane da dama wanda suka yi addu'a ga mamacin...