
A yau Alhamis, Nuwamba 28, 2024— Shugaban jam’iyyar APGA na ƙasa, Sly Ezeokenwa, ya bayyana cewa har yanzu Bianca Ojukwu, ƙaramar ministar harkokin kasashen waje, cikakkiyar ƴan jam’iyyar APGA ce, duk da cewa ta karbi mukamin minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Ezeokenwa ya yi wannan bayani ne a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa jam’iyyar APGA ta ba Ojukwu izinin karɓar wannan muƙami a gwamnatin APC. Ya jaddada cewa Ojukwu ba ta fice daga APGA ba, kuma tana nan daram a matsayin mamba a cikin jam’iyyar.
Shugaban APGA ya ce, “Na kira shugaban kasa kuma na yaba masa a kan wannan naɗin. Ita (Bianca) ƴar jam’iyyar APGA ce, cikakkiyar mambar majalisar amintattu BoT har zuwa yau.”
Bianca Ojukwu ta zama minista ne a lokacin da Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul a watan Oktoba. Duk da cewa ba ta kasance ƴar APC mai mulki ba, Tinubu ya nada ta a matsayin ƙaramar ministar harkokin waje.
Ezeokenwa ya ƙara da cewa wannan naɗin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke jawo ƴan adawa don ba su muƙami a cikin gwamnatin. Wannan mataki yana daga cikin kokarin da shugaba Tinubu yake yi na haɗa kai da sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya.
Bianca Ojukwu, wacce ta kasance sananniyar ƴar siyasa a Najeriya, tana da babban tarihi a cikin jam’iyyar APGA, kuma wannan naɗin na iya zama wani muhimmin mataki a cikin harkokin siyasar Najeriya.
A yanzu, masu ruwa da tsaki a siyasar Najeriya na sa ido kan yadda wannan naɗi zai shafi halin da ake ciki a cikin jam’iyyar APGA da kuma tasirin da zai yi a kan gwamnatin Tinubu.