Bianca Odumegwu-Ojukwu: Labarin Yadda Mahaifinta Ya Koreta Daga Gida

Bianca Odumegwu-Ojukwu, ƙaramar ministar harkokin wajen Najeriya, ta bayyana wani labari mai ban mamaki game da rayuwarta a zamanin matashiya. A taron da aka gudanar a birnin New York, ta yi bayanin yadda mahaifinta ya kore ta daga gida saboda ta shiga gasar kyau.

Bianca ta bayyana cewa, lokacin da ta yanke shawarar shiga gasar sarauniyar kyau, mahaifinta ya nuna fushi da ita, wanda hakan ya sa aka kori ta daga gida na tsawon wata guda. Ta ce, “Iyayena ba su san niyyata ba, ba su tura ni makaranta don na shiga gasar kyau ba.”

Duk da wannan kalubale, Bianca ta jaddada cewa ilimi yana da matuƙar muhimmanci ga kowace mace. Ta yi nuni da cewa, yayin da ta fara samun kuɗi daga gasar, ta fuskanci ruɗani kan barin karatunta na lauya a jami’ar Najeriya, Enugu.

Ta bayyana cewa, “Na yi fama da tunanin barin karatu, amma daga baya na yanke shawarar komawa don kammala karatuna.” Hakan ya zama babban shawara a rayuwarta, inda ta jaddada cewa, “Dole ne ƴan mata su fahimci muhimmancin ilimi da irin ikon da yake da shi a rayuwa.”

Bianca ta kammala da kira ga matasa da su yi ƙoƙarin ci gaba da karatu ko da sun fara samun kuɗi, domin ilimi na ba su damar samun ingantacciyar rayuwa.