Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Bello Turji Ya Yi Barazana Bayan Cafke Babban Abokinsa

Bayan cafke Bago Wurgi, babban abokin aikinsa, hatsabibin dan fashin daji, Bello Turji, ya yi barazana da daukar matakai masu tsauri a wasu yankunan Sokoto da Zamfara. Wannan barazana ta biyo bayan fargabar da aka haifar da cafke Wurgi, wanda ke da muhimmiyar rawa a harkokin tattaunawa da karɓar kudin fansa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Turji ya yi ikirarin zai iya kai hare-hare ko kuma ya yi amfani da dukiyarsa domin tilasta wa hukumomi sakin Wurgi. Ya bayyana cewa yana da adadi mai yawa na dabbobi da zai iya amfani da su wajen wannan shiri.

Kamar yadda aka ruwaito, Bello Turji ya tuntubi manyan sarakuna da shugabannin al’umma, yana mai gindaya sharuda da cewa idan ba a sako Wurgi ba, zai dauki matakai masu tsanani, wanda hakan zai kawo tashin hankali a yankunan gabashin Sokoto da Shinkafi.

Hakanan, an yi arangama tsakanin ‘yan banga da yaran Turji a yankin Fadamar Tara, inda aka samu rahoton cewa yan ta’addan sun yi kokarin kwace iko a yankin, lamarin da ke kara dagula al’amura a yankin. Wannan yanayi na nuna yadda tashin hankali ke kara tabarbarewa a wasu sassan kasar, tare da fargabar al’umma kan abin da zai biyo bayan wannan barazana.