Bello Turji Ya Shirya Sabuwar Makarkashiya Ga Sojoji Bayan Kashe Dansa

Bayan kisan da aka yi wa dansa, shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, ya sake shirya sabuwar makarkashiya ga dakarun sojojin Najeriya a ƙarkashin rundunar Operation Fansan Yamma. Bello Turji ya umarci mayaƙansa da su yi wa dakarun sojoji kwanton bauna a yankin Issah na jihar Sokoto.

Wannan umarnin ya biyo bayan tashe-tashen hankula da sojoji suka yi wajen farautar sa da sauran tsagerun da ke cikin ƙungiyarsa. Masani kan harkokin tsaro a yankin, Zagazola Makama, ya tabbatar da cewa Bello Turji yana amfani da dabarun yaƙin sunƙuru don kawo cikas ga ayyukan da sojoji ke yi.

Majiyoyi sun bayyana cewa, dakarun sojojin sun matsa lamba ga Turji, inda suka kai masa hare-hare da suka jawo mummunan illa ga kungiyar sa. Harin da aka kai masa ya yi sanadiyyar hallaka ɗansa tare da lalata wurin ajiye makamansa.

A halin yanzu, dakarun sojojin suna ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshensa, yayin da Bello Turji ke neman tsira daga wannan matsin lamba. Har ila yau, ya yi barazanar kai hare-hare ga mutanen ƙauyukan da ke kusa da Shinkafi a jihar Zamfara, yana mai gargadi ga duk wanda ya ki bin umarninsa.