
Hukumar tsaro ta Najeriya ta kara tsaurara matakan farmaki kan hatsabibin dan ta’adda, Bello Turji, wanda aka gano yana hijira a sabbin wurare bayan hare-haren da sojoji suka kai masa a jihar Zamfara. An bayyana cewa, Turji ya koma sabon mafaka a gabashin Dutsin Birnin Yaro don tserewa daga tsauraran farmakin da sojoji suka kai a yankin Fakai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Bello Turji ya sauya wurin ajiyar wadanda ya sace zuwa dazukan Dajin Jajjaye, Zaman Gira, Birnin Yaro, da Dogon Karfe. Sabbin ‘yan bindiga sama da 100 sun raka wadanda aka sace, suna daukar matakan tsaro a hanyar Kwanar Jalop dake tsakanin Jangeru da Birnin Yaro.
Hare-haren da sojoji suka kai sun jawo mummunan illa ga Turji, wanda yanzu haka ke neman mafita daga dakarun tsaro. A kwanakin baya, dakarun sojojin sun ruguza wani ginin makaranta da aka yi amfani da shi wajen adana kayan abinci na kungiyar Turji, wanda hakan ya rage musu karfi.
Majiyoyi sun bayyana cewa, Bello Turji na daukar matakai don tsaron wadanda aka sace da karbar kudin fansa, suna kuma neman sabbin hanyoyin da za su tsira daga farmakin da sojoji ke kai musu. Wannan na zuwa ne bayan da Turji ya tura sabbin gungun ‘yan bindiga don kare wadanda aka sace.
Ana ci gaba da kiran gaggawa ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen dakile ayyukan ta’addanci a wannan yanki, musamman a hanyoyin da ‘yan bindiga ke amfani da su don tsira daga hare-haren sojoji.