Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Bello Turji Ya Ci Gaba da Ayyukan Ta’addanci a Jihar Zamfara Duk da Barazanar Sojoji

Bello Turji, shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara, ya ci gaba da kai hare-hare kan matafiya da ƙauyuka a kan hanyar Shinkafi, duk da roƙon da aka yi masa na janye barazanar da ya yi. Wannan lamari ya haifar da firgici ga jama’a da kuma hana zirga-zirgar mutane a yankin.

Hare-haren na zuwa ne bayan wasu shugabannin Fulani sun gana da Bello Turji, inda suka buƙaci shi da ya sake duba shirinsa na tayar da hankula da kuma janye shingen da ya kafa a kan hanyar. Duk da wannan, Bello Turji bai bayar da tabbaci ba, ya bijire ga roƙon da aka yi masa.

Masani kan harkokin tsaro a yankin, Zagazola Makama, ya bayyana cewa hare-haren Turji suna ci gaba da haifar da damuwa a cikin al’umma, tare da jawo hankalin hukumomi kan bukatar daukar matakin gaggawa don dakile wannan matsala.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa ƙarshen Bello Turji na kusa, tare da fatan cewa za a yi nasara wajen kawo karshen ayyukansa na ta’addanci.