Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

“Baza ku wahala a banza ba ” Tinubu ya aika da sako ga Yan Nigeria

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2025 za ta kasance mai cike da dama da arziki ga ‘yan Najeriya. A cikin sakon sabuwar shekararsa, shugaban ya tabbatar wa al’umma cewa dukkan sadaukarwar da suka yi a cikin watanni 19 da ya karɓi mulki ba za ta tafi a banza ba.

Tinubu ya yi wannan bayani a safiyar Laraba, inda ya jaddada cewa gwamnati tana sane da wahalhalun da jama’a ke fuskanta. Ya bayyana cewa dukkanin kokarin da gwamnati take yi na rage matsin tattalin arziki yana samun nasara, tare da rage hauhawar farashi daga 34.6% zuwa 15%.

Shugaban ya gode wa ‘yan Najeriya bisa amincewar da suka ba shi a zabensa na 2023, yana mai cewa wannan amincewa ta ba shi karfin gwiwa. Ya yi alkawarin ci gaba da yi wa al’umma hidima da gaskiya da zuciya ɗaya.

A cewar Tinubu, farashin mai ya ragu a hankali, kuma an samu ribar kasuwanci a tsawon watanni uku a jere. Haka zalika, ajiyar kudin waje ya karu, wanda hakan ya sa Naira ta karfafa kan Dala ta Amurka.

Shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da kasancewa da hakuri, yana mai cewa nasarar da aka samu a gwamnatinsa za ta inganta rayuwar al’umma a cikin shekaru masu zuwa. Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙari wajen magance dukkan kalubalen da suka addabi ƙasar tun bayan hawansa mulki.