
Malamin Jami’ar Uyo, Inih Ebong, wanda aka kori daga aiki ba tare da adalci ba shekaru 22 da suka wuce, ya samu nasara a kotu. Kotun daukaka kara ta Calabar ta tabbatar da hukuncin kotun masana’antu na dawo da shi aiki tare da biyan dukkan hakkokinsa.
Inih Ebong ya gode wa Femi Otedola da lauyan kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong, bisa goyon bayan da suka ba shi a cikin wannan gwagwarmaya. Lauyan Malam Ebong, Nse William, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times cewa wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar, yana mai gode wa Allah.
An kori Ebong daga Jami’ar Uyo a shekarar 2002 bisa zargin barin aiki ba tare da izini ba, duk da cewa ya kasance mai sukar rashin adalci a cikin jami’ar. Yana mai cewa, “Dole ne a biya ni hakkina, ko shugaban jami’ar yana so ko baya so.”
Mista Ebong ya nuna farin ciki da wannan hukunci, yana mai godiya ga dukkan ‘yan Najeriya da suka tsaya tare da shi a cikin gwagwarmayar.
Matar sa, Uduak, ta bayyana cewa wannan gwagwarmayar ta shafi rayuwar su tun lokacin da aka kori malamin, a lokacin da ta haifi ‘yarta ta farko.
Ta ce yanzu haka yarinyar ta na da shekara 21 tana karatun jami’a, kuma dukkan ‘ya’yansu sun kasance masu goyon baya ga gwagwarmayar.