
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana matukar damuwarsa game da yadda ‘yan bindiga suka sake bayyana a dajin Alkaleri, inda ya ce sun karbe ikon yankin. Ya yi kira ga sojojin saman Najeriya da su haɗa kai da sauran hukumomin tsaro don fatattakar ‘yan bindigar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen bikin ‘Ranar Haɗin Kan Sojoji da Fararen Hula’ a hedikwatar sojojin sama da ke Bauchi. Ya yabawa sojojin saman Najeriya bisa nasarorin da suka samu, sannan ya yi Allah wadai da kisan ‘yan banga da ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Mansur.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai wa mafarauta da ‘yan banga hari a safiyar 4 ga Mayu, 2025, lamarin da ya jawo musayar wuta mai zafi. An kashe ‘yan banga tara yayin da mutane 11 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su suka mutu.
Gwamna Bala ya nuna matuƙar baƙin ciki game da kisan ‘yan sa kai tare da mika ta’aziyya ga al’ummar Bauchi. Ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kawo karshen barazanar ‘yan ta’adda.