
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa wasu matafiya ƴan Arewa a jihar Edo. A cikin sanarwa da ya fitar, Sanata Barau ya yi Allah wadai da wannan kisan, yana mai kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kamo masu laifin.
A ranar Alhamis 27 ga watan Maris, 2025, wasu bata gari sun tare matafiyan da ke kan hanyarsu ta komawa Kano, inda suka hallaka su. Sanata Barau ya bayyana wannan kisan a p at L qaa ya dace. Sanatan ya kuma bayyana shirin gabatar da ƙudiri a majalisar dattawa domin tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a wannan mummunan kisan.
Barau ya yi addu’a domin neman rahama ga waɗanda aka kashe, tare da yin kira ga iyalansu da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar an yi musu adalci.