Bankin Duniya Ya Bayar da Bashin $1.5 Billion ga Najeriya Bayan Cire Tallafi


A ranar Litinin, 30 ga Disamba, 2024, Bankin Duniya ya sanar da bayar da bashin $1.5 billion ga gwamnatin Najeriya, bayan aiwatar da wasu muhimman sauye-sauye a fannin tattalin arziki. Wannan bashi na daga cikin mafi sauri da Najeriya ta taba samu, wanda ya biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma gabatar da sabbin kudurorin haraji a gaban majalisar.

Takardun da Bankin Duniya ya fitar sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta sami wannan bashi ne a ranar 13 ga Yuni, 2024, inda aka bayar da rukunin farko na $750 million a ranar 2 ga Yuli, 2024, sannan na biyu kuma a watan Nuwamba na wannan shekara.

Mataimakin shugaban Bankin Duniya, Indermit Gill, ya bayyana cewa duk da cewa wadannan sauye-sauye suna jefa jama’a cikin mawuyacin hali, suna da matukar muhimmanci wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya. Ya kara da cewa wannan mataki na gwamnati zai taimaka wajen inganta hanyoyin samun kudaden shiga da tabbatar da ci gaban kasa.

Duk da haka, cire tallafin mai ya haifar da damuwa a tsakanin ‘yan Najeriya, inda mutane da yawa ke nuna fargaba kan tasirin hakan a rayuwar su. Gwamnati ta yi iƙirarin cewa waɗannan sauye-sauyen zasu taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar a nan gaba.

A halin yanzu, ana fatan wannan bashi zai taimaka wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa da kuma magance matsalolin da suka shafi talauci da rashin aikin yi a Najeriya.