“Babu Wanda Zai Canza Yin Allah,” Gwamna Ya Faɗi Saƙon da Ake Turo Masa a Waya

Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya bayyana cewa ba zai hana kansa barci saboda zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a 2026 ba. Gwamnan ya roki ƴan siyasa su daina turo masa sakonnin tes dake nuna masa akwai matsala a shirinsa na neman tazarce.

Oyebanji ya yi wannan jawabi a taron Yabo da Ibada na wata-wata da aka gudanar a dakin taro na Jibowu da ke gidan gwamnatin jihar Ekiti. Ya bayyana cewa babu wanda zai iya canza abin da Allah ya kaddara, don haka ya buƙaci a kyale shi ya gudanar da aikin da ya dauka na inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Oyebanji ya ce: “Na yi imani da cewa tsarin Allah ya zarce tunanin duk wani ɗan adam, ba zan hana kaina barci ba, komai yana hannun Allah.” Ya kara da cewa duk abin da Allah bai kaddaro wa bawansa ba, ba zai taɓa samun shi ba, kuma idan Allah ya yanke hukunci, babu mai ja da shi.

Gwamnan ya jaddada cewa yana son ƴan siyasa su daina aika masa sakonnin damuwa, yana mai cewa hankalinsa na kan shugabanci da cika alƙawurran da ya ɗauka ga al’ummar Ekiti.

Wannan jawabi na Gwamna Oyebanji ya nuna karfin gwiwar sa da kuma imanin sa a cikin tsarin Allah, yayin da yake fatan ci gaba da yi wa al’umma aiki ba tare da tsangwama daga wasu ƴan siyasa ba.