
Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana dalilan da suka sa sabon kudirin haraji ba zai cutar da Arewa ko talakawa ba. A cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa, Hon. Kofa ya bayyana yadda tsarin sabon kudirin haraji yake da kuma amfaninsa ga al’umma.
Hon. Jibrin Kofa ya ce yana da takaicin ganin wasu ‘yan majalisa suna korafi kan kudirin ba tare da fahimtar abubuwan da ke ciki ba. Ya ce:
“Wallahi, ko kadan babu inda kudirin zai cutar da Arewa ko kuma talaka. Abin da mutane suka damuwa shi ne maganar kaso 60, amma mu jihohin Arewa za mu amfana da wannan kudirin.”
Hon. Kofa ya bayyana cewa kudirin haraji yana da matukar kyau saboda an cire harajin VAT a harkar ilimi, kayan abinci, da bangaren lafiya. Wannan yana nufin cewa:
Cire harajin VAT a kan kayan abinci da ilimi zai taimaka wajen rage matsalolin tattalin arziki da talauci a Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Wannan kudirin haraji na nufin rage farashin kayayyaki ga talakawa, wanda zai inganta rayuwar su.
Hon. Jibrin Kofa ya jaddada cewa babu wata niyya ta cutar da Arewa a cikin wannan kudirin, yana mai cewa ya dade yana aiki a majalisar domin inganta rayuwar talakawa. Ya ƙara da cewa ya kasance mai fafutukar kawo wa Arewa ci gaba, kuma zai ci gaba da yin hakan har abada.