Matsalar Kuɗi: Shugaban NNPCL Ya Kauracewa Majalisa
Shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya fuskanci matsala mai tsanani daga kwamitin binciken asusun majalisar dattawa, bayan da aka bayyana rashin daidaito a cikin bayanan kuɗin kamfanin.Majalisar ta bayyana cewa akwai bambanci na kuɗi na Naira tiriliyan 210 wanda NNPCL ya bayar a rahoton kuɗinsa, amma ba a gabatar da takardun shaida da suka tabbatar da wannan kuɗin ba. Sanatoci sun yi barazanar cewa idan shugaban kamfanin ya gaza bayyana a gaban su, za su iya ɗaukar matakan hukunci da suka haɗa da kama shi da gurfanar da shi a kotu.Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Aliyu Wadada, ya jaddada cewa wannan gayyata ba zaɓi ba ne, yana mai cewa majalisar tana da ƙarfin doka don kiran duk wani jami’in gwamnati da ke guje wa bayar da bayanai da aka buƙata. Ya bayyana cewa ko...








