Boko Haram Sun Kai Sabon Hari a Borno, Sun Yi Barna Mai Tsanani
A ranar 12 ga watan Janairu, 2025, ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani mummunan hari a ƙauyen Shikarkir dake cikin ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno, inda suka yi barna mai yawa. Wannan harin ya biyo bayan wani hari da suka kai a ƙauyen Bamzir, inda suka kashe mutane biyu tare da ƙona wata coci.Mazauna yankin sun bayyana cewa hare-haren Boko Haram sun karu kwarai da gaske, suna haifar da tsoro da rashin tabbas a cikin al'umma. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da cewa sun karɓi rahoton harin, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.Wani mazaunin ƙauyen, Malam Daniel Shikarkir, ya bayyana cewa iyalinsa sun tsira ba tare da rauni ba, amma sun shaida mummunan yanayi da hare-haren ke haifarwa. "Mun ga irin wannan lamari a makwabt...








