Jagoran PDP Ya Yi Gargadi Kan Tsayar da Atiku a Zaben 2027
Cif Bode George, jagora a jam'iyyar PDP, ya yi kira ga jam'iyyar da kada ta sake tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaben 2027. A cewarsa, idan har PDP ta yi wannan kuskure, za ta fuskanci matsala mai girma a zaben shugaban kasa na gaba.Bode George, wanda ya yi magana a cikin wani hira da jaridar The Guardian, ya bayyana cewa Atiku ya riga ya yi rashin nasara a zaben shugaban kasa a lokuta uku, wanda hakan ya nuna cewa ba zai iya kawo canji ba a jam'iyyar. Ya ce, "Atiku ba shi da ra’ayin ci gaban Kudu a zuciyarsa," yana mai zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya raina yankin Kudu.George ya kuma bayyana cewa ba zai yiwu a sake ba wa dan Arewa tikitin takara a zaben 2027 ba, yana mai cewa hakan zai zama zalunci ga yankin Kudu. Ya kara da cewa, "Babu wani dan Kudu ma...








