Uju Kennedy Ohanenye: Tsohuwar Ministar Tinubu Ta Kwana a Hannun EFCC Saboda Zargin Badakala
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, Uju Kennedy Ohanenye, ta kwana a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) bayan da aka tsare ta kan zargin karkatar da kudi. Wannan zargi na da alaka da kudin da aka ware domin tallafawa mata a kasafin kudin shekarar 2023.Hukumar EFCC ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa an karkatar da N138,413,253.89 daga kudin tallafin da aka tanada don gudanar da ayyukan da suka shafi mata. Jami’an hukumar sun yi mata tambayoyi a hedikwatar su, inda suka fara bincike kan rawar da ta taka a cikin wannan badakala.Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa Uju ta isa shelkwatar hukumar da misalin karfe 11:00 na safe, inda aka fara yi mata tambayoyi dangane da zargin da ake yi mata. Wannan lamari yana daga cikin dalilan da su...








