
Atiku da Obi na Shirin Shiga Jam’iyyar SDP Don Tunkarar Tinubu a 2027
A cikin wani sabon ci gaba a siyasar Najeriya, shugabannin adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) domin tunkarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa wakilan Atiku da Obi suna tattaunawa kan wannan shiri.Adebayo ya ce jam'iyyar SDP ta karbi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai daga APC, kuma ta bude kofofinta ga dukkan masu kishin kasa. A wata tattaunawa da ya yi a tashar Channels TV, ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin manyan 'yan siyasa don cimma nasara a zabe mai zuwa.Ya kara da cewa: "Mutane na shiga jam'iyyarmu, kuma muna karbarsu hannu bibbiyu. Idan dukkan 'yan siyasar suka bi dokokin SDP, za mu iya kafa sabuwar tafiya d...