Wuridin biyan bukata
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah Mai Rahma Mai jinkai
Maudu'in mu na yau shine wuridin Biyan Bukata
Abun da Yazo cikin nassi na hadisi ingantace shine yawaita istigfari
Yawaita anbaton istigfari Yana kawo Biyan bukata, da Natsuwa da waraka ga zuciyan Mai anbato
Allah Yana Mai cewa A cikin Alqurani Mai Girma a cikin suratul Nurr Aya ta 10-12
فقلت استغفر ربكم انه، كان غفار
Na ce, ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle shi mai yawan gafara ne.
يرسل السماء عليكم مدرار
Zai aiko da ruwan sama a gare ku mai yawan gaske.
ويمددكم بأموال وبنين ويجعل لكم جنات ويجعل لكم أنهار
Zai albarkace ku da karin dukiyoyi da 'ya'ya, zai kuma yi muku lambuna da koguna.
Wadanan ayoyin Alqurani suna nuna cewa Mai Neman Biyan bukata idan ya yawaita istigfari Allah...








